An kama malamar firamare kan yin lalata da dalibarta

0
96

Wata malamar firamare ta shiga hannun hukuma bisa zargin yin lalata da wata dalibarta mai shekara hudu a Maiduguri, Jihar Borno.

Dubun malamar ta cika ne bayan karamar yarinyar ta bayyana wa iyayenta yadda malamar ta sanya ta a cikin hijabi sannan ta yi lalata da ita.

Mahaifin yarinyar wanda, shi ne ya kai kara ga ’yan sanda, ya ce da farko ya lura yarinyar tana fitsari ja, “Na dauka alama ce ta kamuwa da cuta;  Na kai ta asibiti, suka gaya mana ainihin mene ne matsalar.

“Lokacin da mahaifiyar ta tambaye ta, sai yarinyar ta gaya mata abin da malamar ta yi mata.

“A cewar yarinyar, malamar ta sanya ta ne a cikin hijabinta ta rungume ta, ta ba ta nononta ta tsotse, sannan ta sanya mata yatsa a gabanta.”

Ya ce don haka shi da makwabta suka, “kai rahoto ga ’yan sanda, abin da muke so shi ne a yi mana adalci.”

Kakakin ’yan sanda na Jihar Borno, ASP Sani Kamilu ya shaida mana ranar Asabar a Maiduguri cewa malamar da ke tsare a hannunsu tana koyarwa ne a wata makaranta mai zaman kanta.

Kamilu ya ce a makon da ya gabata ne aka kama malamar kuma rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin3.

Ya ce idan an kammala bincike za a mika karar zuwa Ofishin Kula da Kararrakin Jama’a (DPP) domin daukar mataki na gaba.