‘Yan sanda sun cafke wasu Jami’an EFCC na bogi a Delta

0
104

Rundunar ‘yan sandan Jihar Delta, ta ce ta kama wasu mutane biyar da ake zargin jami’an Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) na bogi.

Wadanda ake zargin sun hada da Prince Allison mai shekaru 29 da George Onyeweagu mai shekaru 29 da Duke Okoro mai shekaru 40 da Joseph Osinachi da kuma Onyocha Sunday mai shekaru 32.

A cewar rundunar ‘yan sandan, wadanda ake zargin sun amince da yi wa mutane fashi a sassa daban-daban na jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Delta, Bright Edafe, a ranar Juma’a, ya ce ayyukan wadanda ake zargin ne ya janyo zanga-zangar #EndEFCC a jihar a watan Oktoba.

Edafe ya bayyana cewa, wani wanda ake zargin ya rutsa da su ya bayyana yadda suka kutsa cikin gidansa da daddare, suka yi awon gaba da shi tare da karbar kudi Naira miliyan biyu da dubu dari biyar da karfin tsiya.

“Shida daga cikin wadanda abin ya rutsa da su kuma sun gano su, daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya bayyana cewa ‘yan kungiyar sun kai farmaki gidansa cikin dare.

“Sun samu shiga harabar ne ta hanyar datse shingen, suka shiga gidansa, suka yi awon gaba da shi da karfi suka tafi da shi cikin wata farar motar kirar Toyota Hiace.

“Sun karbe masa wayoyinsa ta karfi da wasu kayayyaki wanda darajarsu kai N3,700,000, sun yi musayar kudi N2,500,000 kuma suka shaida masa cewa za su sake dawo masa.” In ji kakakin.

LEADERSHIP ta rawaito cewa a watan Oktoba ne wasu matasa a Jihar Delta suka tare wasu hanyoyi a sassan jihar domin nuna rashin amincewarsu da abin da suka bayyana a matsayin kame matasa da jami’an EFCC ke yi.