Gwamnatin Kano ta gargadi kasuwar ƴan lemo a kan tsafta ko ta fuskanci hukunci

0
112

Kwamitin Kar-ta-kwana kan Tsaftar Muhalli na jihar Kano ya baiwa shugabannin kasuwar ƴan lemo wa’adin kwanaki uku da su tsaftace kasuwar ko su fuskanci hukunci.

Shugaban kwamitin, Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin ran-gadi kan Tsaftar muhalli ta kasuwanni, tashoshin mota da guraren aiki a yau Juma’a.

Getso, wanda shi ne Kwamishinan Muhalli na jihar, ya nuna ɓacin ransa a kan yanayin da ya samu kasuwar.

“Mun bai wa shugabancin kasuwar kwanaki uku da a tsaftace ta innkuma ba haka ba to za su fuskanci hukunci. Gwamnatin Ganduje ta baiwa tsaftar kasuwannin abinci muhimmanci sosai.

“Sabo da haka mu na kira ga shugabannin kasuwannin sayar da kayan abinci da su tabbatar da tsaftar muhallansu domin kare lafiyar al’umma,” in ji shi

A nashi ɓangaren, Ciyaman ɗin kasuwar, Safiyanu Abdullahi, ya yi alkawarin tsaftace ta kafin wa’adin kwanaki ukun da a ka bayar ya ƙare.