Buhari ya sha yabo a wajen shugabannin Afirka a Nijar

0
114

A ranar Juma’a ne ake buɗe taron shugabannin ƙasashen Afirka kan hanyar samar da masana’antu da faɗaɗa hanyoyin inganta tattalin arziƙi, a jamhuriyar Nijar.

Sai dai gabanin taron, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da wata hanya mai tsawon kilomita 3.8, a Yamai, babban birnin ƙasar, wadda aka sanya wa sunansa.

Haka nan kuma an yi wani bukin na ƙaddamar da fassarar littafi a kan salon shugabancin Muhammadu Buhari, zuwa harshen Faransanci, wanda Farfesa John Paden na jami’ar Mason University da ke Virgina ta ƙasar Amurka ya wallafa.

Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar ta hannun mai taimaka wa shugaban ƙasar kan yaɗa labaru, Garba Shehu, ta ce Shugaba Buhari ya sha yabo a bakunan shugabannin ƙasashen da suka yi jawabi.

Shugaban jamhuriyar Nijar Mohammed Bazoum ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin “tsayyayen mutum, maras tsoro, mai ƙanƙan da kai, riƙakken ɗan kishin ƙasa kuma masoyin mulkin demokraɗiyya.”

Ya ƙara da cewa “dagewarsa wurin yaƙi da rashawa da tabbatar da kyakkyawan shugabanci, ta sanya ƙaunarsa a zukatan kowa da kowa, yin aiki da mutum mai zurfin tunani irin shi, abin alfahari ne.”

Shi kuwa shugaban Guinea-Bissau, kuma shugaban ECOWAS, Umaro Sissoco Embalo, ya ce ya zama shugaban Guinea ne tare da taimakon Allah da taimakon Shugaba Buhari.

A cewarsa “shekara guda da ta gabata muka raɗa wa wata hanya sunan Shugaba Buhari. Baba, kamar yadda nake kiran shi mutum ne abin koyi, wanda yake a shirye wurin samar da mafita a kowane lokaci.”

A nasa ɓangaren shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby, kamar yadda sanarwar ta ruwaito cewa ya yi “Babu ko shakka Shugaba Buhari jigo ne, wanda ayyukansa da rawar da yake takawa suka sanya duniya take jin maganar nahiyar Afirka.

“Yana bayar da gudumawa wajen ci gaban Afirka ta hanyar kare nahiyar da kuma al’ummarta. Ka koya mana juriya a siyasa.”

Shi kuwa tsohon shugaban jamhuriyar Nijar Muhammadou Issoufou cewa ya yi  “na yarda da kalaman John Paden (mawallafin littafi kan Shugaba Buhari) wanda ya ce Buhari ya yi suna kan haƙuri, da girma, da amana da kuma mayar da hankali wurin tafiyar da aiki.”

“Takensa shi ne Mai gaskiya da amana, kuma babban aboki ne ga jamhuriyar Nijar.”

Tuni dai attajirin nan na Najeriya Mohammed Indimi ya ɗauki nauyin raba wa mahalarta taron kwafe 1000 na littafin kan shugaba Buhari.

BBCHAUSA