Gobara ta tashi a tashar mota ta NTA da ke Filato

0
103

Gobara ta kone fitacciyar tashar mota ta NTA da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato.

Mista Matthew Edogbonya, kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya a Jihar Filato, bai samu damar amsa waya ba.

Amma wani babban jamiā€™in hukumar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da faruwar lamarin a Jos.

ā€œKakaki da sauran manyan jamiā€™an hukumarmu suna wurin da gobarar ta tashi sai dai har yanzu ba su ce komai ba.

ā€œBa za mu iya cewa ga musabbabin faruwar gobarar ba, amma an tura mutanenmu wurin domin kashe ta.

ā€œA halin yanzu, ba za mu iya cewa ga adadin abubuwan da suka salwanta ba.

ā€œAbin da muka fi damuwa da shi a yanzu shi ne kashe gobarar saboda kada ta lalata dukiya ko salwantar rayukan mutane,ā€ in ji shi.

NAN ta ruwaito cewa tashar motar na daura da gidan talabijin na NTA da ke Jos, wanda ke kan hanyar Yakubu Gowon, Jos.