Mun kammala bincike kan fasa Kurkukun Kuje – Aregbesola

0
104

Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya, Rauf Aregbesola, ya ce sun kammala bincike tsaf kan fasa gidan gyaran hali na Kuje da ’yan ta’adda suka yi a watan Yulin da ya gabata.

Ya ce kodayake an kama wasu daga cikin tserarrun fursunonin da dama, har yanzu wadanda suka gudun na da matukar yawa.

A ranar biyar ga watan Yulin bana ce dai wasu ’yan ta’adda suka fasa gidan yarin na Kuje da ke Abuja, inda akasarin fursunonin gidan, ciki har da dukkan ’yan Boko Haram din da ake tsare da su a ciki, suka tsere.

Aregbesola ya bayyana haka ne ranar Talata a Abuja, yayin jawabi ga ’yan jarida karo na hudu kan nasarorin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ma’aikatarsa.

“Muna da matakai daban-daban na bincike, mun kammala namu kuma mun tura da rahoto, amma kasancewar abu ne da ya shafi tsaro, ba zai yiwu mu bayyana komai ba a nan. Abin da kawai zan iya cewa ke nan,” inji shi.

A cewar Minista Aregbesola, babban abin da za a ci gaba da tuna Buhari da shi ko bayan ya bar mulki shi ne na tabbatar da cewa babu wani bangare na Najeriya da ke karkashin ikon kungiyar Boko Haram.

A wani bangaren kuma, Ministan ya alakanta tsaikon da ake fuskanta wajen samun fasfon Najeriya ga rashin isassun cibiyoyin daukar bayanan mutane.

Sai dai ya ce gwamnati na matukar aiki wajen ganin ta bude karin wuraren yin fasfo din a fadin Najeriya.