Qatar 2022: Saudiyya ta lallasa Argentina a gasar cin Kofin Duniya

0
126

A ci gaba da fafata wasanni Gasar Cin Kofin Duniya da take gudana a kasar Qatar, Saudiyya ta lallasa Argentina, kasar da Lionel Messi yake buga wa wasa da ci biyu da daya.

Argentina ta yi rasin nasara a hannun Saudi Arabia da ci 2-1 a wasan farko a rukuni na uku a Gasar Cin Kofin Duniya da suka kara ranar Talata a Qatar.

Minti 10 da fara wasa Argentina ta ci kwallo ta hannun Lionel Messi a bugun fenareti.

Kyaftin din Argentina ya zama na biyar da ya ci kwallo a gasa hudu a kofin duniya, wanda ya yi hakan a 2006 da 2014 da 2018 da kuma 2022.

Wadanda ke rike da tarihin wannan bajintar sun hada da Pele da Uwe Seeler da Miroslav Klose da kuma Cristiano Ronaldo.