Ƴan sanda sun tsare mutumin da ya kulle matarsa a daki a Yobe

0
146

Rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Yobe ta ce tana ci gaba da bincike kan wani mutum, wanda ake zargi da kulle matarsa a ɗaki na tsawon lokaci ba tare da kulawa ba.

Tuni dai matar, mai suna Sadiya Salihu, wadda ƴar asalin jihar Kano ce ta rasu a wani asibiti da ke Kano bayan ta sha fama da jinya.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem, ya shaida wa BBC cewar yanzu haka suna tsare da mijin matar, kuma suna shirin gurfanar da shi a gaban kotu.

A cewarsa “a yanzu da nake magana mun riga mun fara bincike.”

Sai dai ya ce mutumin da ake tuhuma ya musanta zargin da ake masa a lokacin da ƴan sanda suke yi masa tambayoyi.

Ya kara da cewa rundunar ƴan sanda tana ci gaba da riƙe shi saboda irin bayanan da take da su.

Haka nan Mr Dungus ya ce rasuwar matar za ta iya sauya irin tuhume-tuhume da za a gabatar gaban kotu.

A cewarsa rahoton da likita zai bayar ne zai tantance yadda tuhumar za ta kasance.

A yanzu iyaye da dangin matar na zaman makoki bayan rasuwarta ‘sakamakon bakar azabar da ta sha a lokacin da take tsare’.

Daya daga cikin ‘yan uwan matar Aisha Salihu, ta shaida wa BBC cewa bayan sun dauko ‘yar uwar tasu daga Yobe sun dawo ita gida Kano don yi mata magani, sun kai ta asibiti amma duk wani gwajin cuta da aka yi mata ya nuna ba ta dauke da kowanne ciwo.

Ta ce likitoci sun shaida musu cewa akwai yunwa a tare da ita da kuma matsananciyar damuwa.