Harbin ma’aikaciyar jinkai: Zulum ya jajanta wa majalisar dinkin Duniya

0
113

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya aika wa Majalisar Dikin Duniya sakon jaje bisa kisan wata ma’aikaciyar jinkai ’yar kasar Habasha, Alem da wani soja ya yi.

Gwamnan ya aika da sakon ta’azziyar ne ta wata wasika da ya aikewa Mista Matthias Schmale, Wakilin Majalisar a Najeriya.

Zulum ya bayyana matukar bakin ciki da alhinin abin da ya faru na harbin da sojan ya yi a garin Dambowa a ranar Alhamis.

Harbin dai ya halaka Misis Alem Museta da kuma abokan aikinta na kungiyar agaji ta Likitoci mai suna ‘Medicine de Monde’.

“Ina mika ta’aziyyata ga iyalan wannan mata da ta rasu, da kuma sauran iyalan sojojin da suka mutu yayin da suke kokarin rike wannan soja daga aikata wannan danyen aiki”. In ji gwamna Zulum.

Gwamnan ya kuma ce, an garzaya da matukin jirgin da shi ma harbin ya rutsa da shi asibiti, yana kuma samun kulawa, kuma gwamnati za ta ci gaba kulawa da shi har sai ya samu lafiya.

Sannan gwamnan ya ce, su na nan, su na binciken lamarin, ya kuma tabbar da cewa za su dauki matakin kula da lafiyar kwakwalwar sojojin da ke bakin daga.

Ana zargin sojan ya yi harbin ya larurar tabin hankali.