Wani dalibi ya kashe kansa saboda budurwarsa ta ki amsar soyayyarsa

0
108

Wani ɗailibin ajin ƙarshe a kwalejin fasaha ta tarayya ta Oko da ke jihar Anambra ya kashe kansa saboda budurwarsa ta ƙi amsar tayin soyayya da ya yi mata.

Wata majiya ta bayyana wa Jaridar Daily Trust cewa ɗalibin ya ɗauki matakin ne bayan da budurwar da yake matuƙar so ta ce masa ya je ya nemi wata budurwar.

Rahotonni sun ce ɗalibin na koyon sanin makamar aiki a shirye-shiryen kammala karatun nasa.