Mai alkawarin azurta ’yan Najeriya 100m ya talauta 133m – Shehu Sani

0
162
Sanata Shehu Sani ya goranta wa Gwamnatin Shugaba Buhari kan ’yan Najeriya miliyan 133 da ke fama da fatara, duk da alkawarin ta na fitar da ’yan kasar miliyan 100 daga kangin talauci.

A sakonsa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shehu Sani ya ce maimakon azurta ’yan kasa gwamnati ta buge da jefa miliyan 133 daga cikinsu a kangin talauci.

A cewarsa, “Sun yi alkawarin raba mutum miliyan 100 da talauci, sai ga shi a hukumance sun jefa mutum 133 ciki.”

A baya, Shugaba Muhammadu Buhari ya  bayyana tsare-tsaren da gwamnatinsa ta shirya don cire ’yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci ya zuwa 2030.

A watan Satumba, Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Kwadago da Raba Ayyuka, Kachollum Daju, ta fada wa manewa labarai cewa za a iya cimma wannan manufa muddin masu ruwa da tsaki suka yi aikinsu yadda ya kamata.

Sai dai kuma, a ranar Alhamis Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta ba da sanarwar ’yan Najeriya miliyan 133 ne ke fama da talauci, wanda shi ne kwatankwacin kashi 63 na yawan al’ummar kasar.