Ta tabbata an sallami shugaban hukumar NYSC

0
170
Ministan Wasanni da Harkokin Matasa, Sunday Dare, ya tabbatar da sallamar Darakta Janar na Hukumar Kula da Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC), Birgediya-Janar Mohammed Fadah.

A safiyar Juma’a ne ministan ya tabbatar mana da sallamar, wadda tun kafin wayewar gari kafofin sada zumunta suke ta yadawa.

Ga sakon da wakilinnmu ya tura masa na neman sanin hakikanin labarin, Ministan ta ce, “gaskiya ne,” an sallami shugaban na NYSC.

Aminiya ta samu rahoto cewa an umarci Birgediya-Janar Mohammed Fadah ya mika duk kayayyakin Hukumar NYSC da ke hannunsa ga jami’in da ke biye da shi a matsayi, wanda shi ne zai kasance Mukaddashin Darakta-Janar na hukumar.

Tun da farko wata majiya a Fadar Shugaban Kasa ta tsegumta wa wakilinmu cewa shugaban na NYSC  na dab da rasa kujerarsa, bayan ministan ya nuna rashin gamsuwa da kamun ludayinsa.

Majiyar ta ce, “Abin ya kai ga ministan ya kai korafi game da dabi’un wasu manyan mutane; Na sa ba wannan ne na karshe ba.