Lauyoyin Arewa sun zargi EFCC da nuna wariya kan wadanda ake zargi da badakalar kudade

0
115

Lauyoyi a Arewa da ke karkashin kungiyar ‘Arewa Lawyers Progressives Forum’ sun zargi Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), da cin zarafin ‘yan siyasa, baje kolin muradinsu a kafafen yada labarai gami da nuna wariya wajen zaben wadanda ake zargi tare da maida hankali kan wasu da lullube wasu a kasan tabarma.

A wata sanarwar manema labarai da Abubakar Kurawa a madadin lauyoyin kungiyar, ya ce, sun gano cewa akwai kesa-kesan da ake rufewa a kuma yi ta ruruta wasu kuma hakan bai rasa nasa ba da siyasa duk kuwa da cewa akwai tilin kesa-kesan rashawa da dama a jiha.

Kungiyar ta ce, akwai manya-manyan kesa-kesan rashawa da zagon kasa da hukumar ta yi gum da su duk kuwa da cewa ya kamata a ce suna karkashin binciken hukumar, a maimakon hakan hukumar ta bage da matsa lamba ga wasu daidaiku mutane.

Daga bisani kungiyar ta yi kira ga Shugaban hukumar na EFCC da ya ke tabbatar da ana bibiyar kesa-kesai yadda suka dace ba tare da nuna wariya da son kai ba.