Za a sayo wa makarantun FGC 18 motocin daukar marasa lafiya

0
133
Gwamnatin Tarayya za ta sayo motocin jigilar marasa lafiya guda 18 don amfanin makarantun sakandare na  kwana a fadin Najeriya.

Majalisar Zartaswa ta Kasa ta kuma amince a zamanta na ranar Laraba a kashe Naira biliyan N3.269 wajen katange Jami’ar Usman Danfodiyo ta Sakkwato (UDUS).

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya ce, an ba da kwantaragin gina katangar ne ga kamfanin Amis Construction Nigeria Limited.

Kazalika, ministan ya ce, gwamnati ta sake amincewa da kashe biliyan N5.1 wajen buga muhimman takardu da sauransu wa Hukumar Shirya Jarrabarawa ta Kasa (NECO).

Za kuma a kashe N2.bn wajen saya wa Hukumar Kiyaye Hadurra motocin aiki guda 145, inji mai magana da yawun Shugaban Kasa, Femi Adesina.