Rikici ya dabaibaye jam’iyyar NNPP a wasu jihohin Arewacin Najeriya

0
137

Rikicin cikin gida na ci gaba da turnuƙewa a rassan jam’iyyar NNPP, na wasu jihohin Arewa maso yammacin Najeriya.

Hakan na zuwa ne yayin da babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2023 ke ci gaba da matsowa.

Rikicin a yanzu haka ya yi sanadiyyar korar wasu jiga-jigan jam’iyyar yayin da wasu kuma suka sauya sheƙa.

An kori shugaban jam’iyya da ɗan takarar mataimakin gwamna a Sokoto

Rikicin da ya turnuƙe  jam’iyyar ta NNPP a Sokoto ya yi sanadin korar wasu jiga-jiganta, ciki har da shugaban jam’iyyar na jiha da kuma mataimakin ɗan takarar gwamna.

Malam Muhammad Abdullahi Bancho dan kwamitin zartarwar jam`iyyar NNPP ne a jihar Sokoto ya ce “gaskiya ne mun kore su saboda mun kama su suna ‘anti-party’”

Ya ƙara da cewa “mun zauna da su kuma sun tabbatar mana lallai sun aikata haka.”

Reshen jihar Sokoto na jam`iyyar ya ce ya daɗe da fahimtar take-taken mataimakin ɗan takaranta na muƙamin gwamna, wato Ibrahim Ango da shugaban jam’iyyar na jiha, Bello Ahmed da wani shugabanta na shiyya.

Kuma jam’iyyar ta ce ta gano cewar suna ƙoƙarin raba kafa ne da wata jam’iyya da nufin ɓata mata tafiya a jihar ta Sokoto.

Ofishin jam’iyyar na ƙasa da ke Abuja ma ya tabbatar da korar jiga-jigan jam’iyyar na jihar Sokoto.

Farfesa Rufa’i Alkali wanda shi ne shugaban jam’iyyar na ƙasa ya shaida wa BBC cewa yanzu haka suna jiran cikakken rahoto ne kan abin da ya faru.