Za mu cire tallafin man fetur a 2023 – Gwamnatin tarayya

0
141

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta bayyana cewar gwamnatin tarayya za ta daina biyan kudin tallafin man fetur a watan Yunin 2023.

Zainab, ta bayyana haka ne a lokacin da ta gana da manema labarai a Abuja, babban birnin tarayya bayan kammala taron tattalin arziki na kasa karo na 28.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya rawaito cewa biyan tallafin kudin man fetur ya lashe Naira tiriliyan 2.565 tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2022.

Har wa yau, kuma a cikin kasafin kudin bana, gwamnatin tarayya ta kiyasta za ta kashe Naira tiriliyan 3.3 wajen biyan tallafin man fetur din tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2023.

Ta kara da cewa kudin tallafin man fetur din na kawo wa kasafin kudin gibin da dole sai an ciwo bashi kafin cike shi.