Sufeton ‘yan sanda ya ba da umarnin tsaurara tsaro a hanyar Legas zuwa Ibadan

0
112

Sufeto Janar na ‘yansanda, IGP Usman Baba, ya bayar da umarnin tsaurara matakan tsaro a kan titin Legas zuwa Ibadan mai cike da cunkoson jama’a, biyo bayan yawaitar sace-sacen jama’a da rashin tsaro a hanyar.

Mai magana da yawunsa, Olumuyiwa Adejobi, ya ce hakan ya biyo bayan bayanan da aka samu na tsaro a kan babbar hanyar daga kwamishinonin ‘yan sanda masu kula da jihohin Legas, Ogun da Oyo.

Ya ce babban sufeton ‘yansandan ya ba da umarnin sake fasalin jami’an tsaro cikin gaggawa a kan babbar hanyar domin samar da isassun jami’ai don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a kan hanyar tare da dakile sace-sacen mutane da sauran munanan abubuwan da ke faruwa.

Hakazalika, IGP din ya jaddada cewa, hukumar ‘yansanda ba ta damu da matsalolin tsaro da ake fama da su a hanyar Legas zuwa Ibadan ba, sai dai sun shagaltu wajen magance matsalar tsaro da dabarun kawar da barazanar da ke kan hanyar; don haka ne aka yi ta tantance hanyar.

Sufeton ya kuma yi alkawarin samar da isassun kayan gudanar da aiki ta hanyar fasahar kere-kere da kadarorin aiki ga kwamishinonin ‘yansanda masu kula da jihohin Legas, Ogun, da Oyo.

 Hakazalika, ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya masu kishin kasa, musamman masu amfani da hanyoyin, mafarauta, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da ke bin hanyar da su rika tona asirin barayin da suke addabar ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba a kan hanyar da kuma sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su.

‘Yansanda da sauran jami’an tsaro domin za su kama tare da kuma gurfanar da duk mai laifin da aka kama a hanyar a gaban kuliya.