Kamfanin Amazon zai sallami ma’aikatansa 10,000 daga aiki

0
107

Kamfanin Amazon na shirin sallamar kusan ma’aikata 10,000, kamar yadda jaridar New York Times ta rawaito a ranar Litinin.

kamfanin wanda ke da ma’aikata miliyan 1.54 a duk fadin duniya a karshen watan Satumba.

Rahoton Times ya ce wuraren da abin ya shafa sun hada da sashen na’urori na Amazon, tallace-tallace da albarkatun dan adam.

Ma’aikatan da aka kora za su fuskanci tashin hankali biyo bayan sallamarsu daga aiki.

Biyo bayan tabarbarewar tattalin arziki, makonni biyu da suka gabata Amazon ya ba da sanarwar dakatar da daukar ma’aikata kuma tuni ma’aikatansa suka ragu idan aka kwatanta da farkon shekara.