Sadique Abubakar ya bai wa dalibai 201 tallafin karatu a Bauchi

0
134
Dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a Jihar Bauchi, Air Marshal Sadique Baba Abubakar (mai ritaya), ya bai wa dalibai 201 tallafin karatu a Kwalejin Kiwon Lafiya da ke jihar.

Da yake jawabi yayin gabatar da tallafin karatu ga daliban da suka amfana a ranar Litinin a harabar kwalejin, Sadique Abubakar, ya shawarci daliban da su rika daukar karatunsu da muhimmanci ta yadda za su yi fice kuma su zama masu amfani ga al’umma.

Ya ce “Ilimin kiwon lafiya na da matukar muhimmanci ga rayuwar al’umma, don haka ku dauki karatunku da muhimmanci.”

Abubakar ya caccaki gwamnatin mai ci kan yadda ta ki bai wa fannin ilimi kulawa, inda ya kara da cewa idan aka zabe shi zai ci gaba da tallafa wa marasa galihu da marasa karfi a cikin al’umma domin samun ilimi mai inganci.

Abubakar ya kuma nuna bacin ransa ga gwamnati mai ci kan watsi da yarjejeniyar tallafin ilimi da gwamnatin da ta shude ta yi.

A cewarsa, “Abun bai dace ba, ilimi ba abu ne da gwamnati ita kadai ba za ta iya ba. Idan aka zabe mu, zamu sake duba batun ta yadda za a sake duba yarjejeniyar ilimi.”