Majalisar dokokin jihar Ekiti ta zabi sabon kakaki

0
106

Mambobin Majalisar Dokokin Jihar Ekiti sun zabi sabon Kakaki wanda ya kasance Rt. Hon. Gboyega Aribisogan, mamba da ke wakiltar mazabar Ikole a jihar.

An zabi Aribisogan, ne a yayin zaman Majalisar na ranar Talata domin ya maye gurbin tsohon Kakakin Majalisar Rt. Hon. Funminyi Afuye, wanda ya mutu a makon da ya gabata sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita.