Jiragen yakin Amurka 2 sun yi taho mu gama a sararin samaniya

0
137

Wasu jiragen yakin sojin Amurka sun yi hatsari bayan sun yi taho-mu-gama suna tsaka da atisaye a sararin samaniya a jihar Texas ta Amurka.

Hatsarin ya faru ne ranar Asabar, inda jiragen suka fado kasa suna ci da wuta, sannan suka tirnike da wani bakin hayaki.

Har yanzu dai babu tabbaci kan ainihin yawan mutanen da suka jikkata ko suka mutu a hatsarin.

Lamarin dai ya ritsa da wani jirgi kirar Boeng B-17, samfurin wanda aka yi Yakin Duniya na Biyu da shi da kuma wani samfurin Bell P-63, wanda ke shawagi a sararin samaniyar babban filin jirgin sama na birnin Dallas a jihar ta Texas, kamar yadda Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka (FAA) ta tabbatar.

Hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa tuni jami’an bayar da agajin gaggawa suka isa wajen, kodayake ta ce babu tabbacin yawan mutanen da ke cikin jiragen guda biyu.

Shugaban sashen da ke kula da jiragen yakin da aka yi yakin duniyar da su na Rundunar Sojin Saman Amurka, Hank Coates, ya shaida wa wani taron manema labarai cewa jirgin kirar B-17, galibi yakan ci mutum hudu zuwa biyar.

Shi kuwa P-63, a cewarsa, matuki daya ne yake tuka shi, amma ya ki amincewa ya bayyana aininin mutanen da ke cikin jirgin yayin hatsarin, ko sunayensu ko kuma ma halin da suke ciki.

Wasu hotuna sun nuna wasu sassan jirgin a wajen da harin ya auku a wani waje mai ciyayi a harabar filin jirgin saman.

Hukumar Kashe Gobara ta birnin na Dallas ta shaida wa jaridar ‘The Dallas Morning News’ cewa hatsarin bai jikkata kowa ba a a inda ya fado kasa.