Ba zan rika fita waje ganin likita ba idan na zama shugaban kasa – Kwankwaso

0
135
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa wajen ganin bai rika fita kasashen waje domin ganin likita ba idan aka zabe shi Shugaban Kasa a 2023.

Kwankwaso, wanda tsohon Gwamnan jihar Kano ne ya yi alkawarin ne lokacin da yake jawabi a taron tattaunawa da gidan talabijin na Channels ya shirya wa ’yan takarar da daren Lahadi.

Ya yi kalaman ne kusan daidai lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga Landan domin ganin likitoci, inda ya shafe kusan mako biyu.

Da aka tambaye shi tanadin da ya yi wa bangaren lafiya na Najeriya idan ya zama Shugaban Kasa, Kwankwaso ya ce, “Zan yi iya duk kokarina wajen ganin ban fita kowace kasa ba domin ganin likita.

“Koma-bayan da muke da shi a yau, wadanda muka yi alkawarin magancewa, suna shafar dukkan bangarori, kuma ina farin cikin sanar da ku cewa za mu fara da fannin ilimi, kamar yadda muka yi a Kano.

“Mun gina makarantu guda biyar a karkashin Ma’aikatar Lafiya – makarantun jinya guda biyu da na unguwar zoma guda biyu da kuma Kwalejin Fasahar Lafiya.

“Mun aike da mutane ketare, sannan mun ba su tallafin karatu domin su karanci fannin likitanci. Mun kuma inganta dukkan manyan asibitocin jihar Kano,” inji shi.

Tsohon Ministan Tsaron na Najeriya ya kuma ce zai dauki isassun ma’aikatan da za su yi aiki a daidai lokacin da suke tururuwar barin kasar zuwa ketare.

Ya kuma sha alwashin cire duk wasu abubuwa da suke zame wa ma’aikatan lafiya na Najeriya karfen kafa, suna hana su yin fintinkau.