FIFA ta gargadi kasashe a kan sa siyasa a harkar kwallon kafa

0
112

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta aike wa duka kasashe 32 da za su halarci gasar cin kofin duniya wasika, tana neman su mayar da hankali kan kwallon kafa, biyo bayan ce-ce-ku-cen da ake ta yi daf da fara gasar.

Mai masaukin baki Qatar na ta fama da suka kan matsayarta game da auren jinsi, da yancin dan adam da kuma yadda take tafiyar da lamarin ‘yan cirani da ke aikatau, wadanda akayi zargin an ci zarafin su.

Wasikar ta yi gargadin cewa bai kamata a a rika jayayya a kwallon kafa ba, kan wani tunani ko kuma siyasa, kuma ba a amfani da ita wajen gyaran halayya sai dai wasu ‘yan wasa sun shirya gudanar da zanga-zangar lumana gabanin fara wasannin.

Kyaftin din Ingila Harry Kane da wasu kyaftin tara na kasashen Turai za su sanya kambi nuna kauna sannan ‘yan wasan Australia sun saki wani bidiyo suna shawartar Qatar da ta yi watsi da dokarta akan sha’anin auren jinsi.

Birnin Paris na Faransa da wasu sauran birane sun ce ba za su haska wasannin kofin duniyar ba a manyan majigi, duk da cewa Faransan ce ke rike da kofin sannan ‘yan wasan Norway sun sanya riga da ke magana kan hakkin dan adam a ciki da wajen filin kwallo, ko da yake tawagar ba ta yi nasarar halartar gasar da za a yi a kasar ba.