Zabar Gawuna da Garo babban alheri ne ga jihar Kano – Engr Bashir Kutama

0
160

Daga Abubakar Abdulkadir, Kano

Shugaban karamar hukumar Gwarzo a Jihar Kano Injiniya Bashir Abdullahi Kutama yace karkashin jagorancin sa, karamar hukumar ta sami gagarumin ci gaba na ayyukan raya kasa bisa kulawar tsohon kwamishinan kananan hukumomi kuma dan takarar mataimakin gwamna Alhaji Murtala Sule Galadima Garo.

Shugaban karamar Hukumar ta Gwarzo yace sun shimfida ayyulan alheri ga daukacin yankin  a fannoni daban-daban da suka hada da ilimi da kiwon lafiya da hanyoyi da sha’anin tsaro da kuma tattalin arzikin yankin.

Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya bayyana hakan ne yayin wata ganawar sad a manema labarai, a wani bangare na ci gaban da yakin neman zaben gwamnan Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakin sa Alhaji Murtla Suke Garo a zaben shekara ta 2023.

Yace babban abinda yake alfahari das hi game da Murtala Sule Garo shi ne iya mu’amala da kuma yadda ya rika dawainiya da kananan hukumomin Kano, inda kowacce aka bata daidai- iko da dammar da ta kamata da kuma abub uwan day a taimaki al’umma kai tsaye.

‘bin Alfaharin na gaba shi ne harkar tsaro, idan ka dauki kananan hukumomin mu musamman karamar hukumata ta Gwarzo muna a kan babban titi wanda ya hada jihar Zamfara da Katsina da jihar Kebbi kuma gamu kusa da kusa da bangare day a fi matsala a jihar Katsina, amma cikin ikon Allah da kwarewar wannan bawan Allah (Murtala Garo) tashin farko a zuwa na a matsayin shugab an karamar hukuma ya fara zaburar da mu kan cewar mu samar da dukkanin rukuni da dukkanin wani abu da zai tallafi dukkanharkar jami’an tsaro a wannan karamar hukuma’’

‘’Ina tabbatar maka bisa kulawar sad a umarni nasa muka samar da hukumar  Road safety a wannan karamar hukuma wanda command ne guda a cikin garin Gwarzo, mun samar da zonal command na NDLEA wanda kusan kananan hukumomi 11 na wannan yanki yake karkashin wannan command, muka samar da ofishi na DSS wand azan ce maka daga babban ofishin su  na jiha sai wannan’’

‘’ Sannan mun samar da shalkwata ta JTF wadda take kula da dukkanin yammacin jihar Kano, kuma tana nan a wannan gari namu na Gwarzo, to ka ga dukk hangen nesa ne irin nasa da kuma tunanin kan cewar ita karamar hukumar Gwarzon ta zama murfin Kano ta yamma, to tana da bukatar bata kyakkyawan tsaro’’

Shugaban karaar hukumar ta Gwarzo ya kara da cewar, su kan su basu fahimci muhimmancin abin ba, amma Murtala Sule Garo ya matsa musu said a aka tabbatar da ganin tsaro ya inganta a wadanan yankunan, abinda ya sanya jihar Kano kasancewa jihar da ta fi zaman lafiya da tsaro.

Injiniya Bashir Kutama y ace dukkan wadanan nasororin da suka cimma karkashin kulawar Murtala Sule Garo sun samu ne bisa sahalewa da dama da mai girma gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Gnduje ya bas hi yayin da yake kwamishinan kananan hukumomi.

Kasancewar sa sakataren kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta jihar Kano , ya ce domin kara karfafa waccan yunkuri na tabbatar da tsaro, an dauki mutane dari biyu a kowacce karamar hukuma domin tallafawa ‘yan sintiri, wanda wannan kadai ya isa a jinjinawa Gwamna Ganduje da Murtala Sule Garo bisa samar da ayyukan yi ga matasa.

Shugaban karamar Hukumar ta Gwarzo yace duba da irin wadannan ayyukan alheri, abu ne dake haskawa al’ummar jihar Kano cewar, zabar Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sue Garo a matsayin gwamna da mataimaki zai kasance babban alheri ga Kanawa.

Yace dukkan mutanen biyu, sun yi aiki a matakin gwamnati mafi kusa da al’umma watao kananan hukumomi har suka kai matakin da suke kai a yanzu, inda yashawarci al’ummar Kano su zabi wadannan bayin Allah domin dora Kano a kan turbar ggarumin ci gaba, saboda haka zaben Gawuna da Garo babban alheri ne ga jihar Kano.

Sannan ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar APC a dukkan matakai da su guji shiga duk wani nau’I na tada fitina da husuma, kasancewar baya cikin akidin jam’aiyyar domin a gudanr da zabukan badi cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.