‘Yan sanda sun cafke ‘yan kungiyar asiri 3 a Ondo

0
106

Jami’an rundunar ‘yansandan Jihar Ondo sun kama wasu matasa uku da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne.

Wadanda ake zargin sun hada da Adeyeye Deji, Adesuyi Damilola da kuma Abiodun Lekan, an kama su ne a lokacin da suke yunkurin kai hari ga mambobin jam’iyyar Odua People’s Congress, OPC, a Akure, babban birnin jihar.

An tattaro cewa mutanen ukun na cikin kungiyar asiri mai suna Eiye Confraternity.

An ce sun kai farmakin ramuwar gayya ne a lokacin da aka kama su a Abusoro da ke yankin Ijoka a Akure.

Yayin da ta ke gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar ‘yansandan Nijeriya da ke Akure, kakakin ‘yansandan, Funmilayo Odunlami, ta ce tawagar jami’an ‘yansandan ta kama wadanda ake zargin.

A cewar kakakin, an gano bindigogi biyu na gida daga maboyar ‘yan kungiyar.

Ta ce, “A ranar 29 ga Oktoba, 2022, da misalin karfe 12:00 na dare, bayan da aka samu labarin cewa wasu ‘yan kungiyar asiri na shirin kai wa wasu ‘yan kungiyar OPC hari a Abusoro, titin Ijoka, Akure, da nufin daukar fansa.

“Tawagar ‘yansanda daga SWAT ta koma wurin da lamarin ya faru kuma ta kama wadanda ake zargin: Adeyeye Deji, Adesuyi Damilola da kuma Abiodun Lekan.