EFCC ta mayar wa CBN kudi sama da naira biliyan 19 da aka boye

0
112

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta ce ta mayar da kudaden ceto tattalin arziki na naira biliyan 19.3 ga babban bankin Najeriya wanda ake zargin gwamnatin jihar Kogi ta boye .

Tun farko hukumar ta bayyana cewa gwamnatin Yahaya Bello ta boye kudin a asusun wani banki.

Gwamnatin jihar Kogin ta musanta zargi kuma ta zargi EFCC da kokarin shafa mata kashin kaji.

Sai dai a wata sanarwa a ranar Juma’a ,kakakin hukumar, Wilson Uwujaren, ya ce an tura da kudaden zuwa babban bankin.