EFCC ta daukaka kara kan hukuncin aike da shugabanta gidan yari

0
113

Shugaban Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa a jiya ya ce hukumar ta daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun birnin tarayya ta yanke na tsare shi a gidan yarin Kuje.

Bawa ya bayyana haka ne a harabar majalisar dokokin kasar nan yayin da yake amsa tambayoyi jim kadan bayan ya gurfana gaban kwamitin majalisar kan laifuffukan cin hanci da rashawa domin kare aiwatar da kasafin kudin 2022 da kuma kudirin kasafin kudin 2023.

“Mun riga mun daukaka kara a kan hakan don haka za mu ba da damar bin tsarin doka ya yi tasiri,” in ji shi.

A jiya ne mai shari’a Chizoba Orji na babbar kotun birnin tarayya Abuja, ya yanke wa shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta’annati (EFCC) Abdulrasheed Bawa hukuncin tsarewa a gidan yari dangane da gazawar hukumarsa na kin bin umarnin kotu.

A hukuncin da kotun ta yanke, ta ce “Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ya yi watsi da umarnin da kotu ta bayar a ranar 21 ga Nuwamba, 2018, inda ta umarci Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, Abuja da ta mayar wa mai nema motarsa mai suna Range Rover da kuma kudi N40, 000,000 (Naira miliyan arba’in).

Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar, ta dora alhakin hukuncin da kotun ta yanke kan wasu bayanai da ba su dace ba, inda ya ce tuni shugaban ya saki motar da ake magana a kai ya kuma amince da sakin kudin.

Tuni dai hukumar ta shiga rudani tun bayan aike da shugaban nata gidan yari.

Sai dai EFCC na ganin akwai kuskure wajen bayyana wasu bayanai wanda suke da alaka da aike da shugaban nata gidan yari.