Ambaliyar ruwa: Aisha Buhari ta raba tallafin N10m a Binuwai

0
133

Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta bayar da tallafin naira miliyan 10 domin rage radadin mutanen da suka fuskanci ambaliyar ruwa a Jihar Binuwai.

Aminiya ta ruwaito cewa, Aisha Buhari ta ba da tallafin ne ta hannun mai dakin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Sanata Oluremi Tinubu.

Bayanai sun ce Aisha Buhari ta ce a raba tallafin a tsakanin mutane 200 da ambaliyar ruwa ta janyowa asarar muhallai da dukiya a Makurdi, babban birnin jihar.

Tuni dai Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (SEMA) a Binuwai, ta ce an raba tallafin ga wadanda ibtila’in ambaliyar ya rutsa da su.

Babban Sakataren SEMA, Dokta Emmanuel Shior ya ce sun raba kudin ne ga kauyuka biyar da abin ya fi shafa a Makurdin.