Sarkin Arewan Bauchi ya rasu

0
111
Sarkin Arewan Bauchi

Iyalan sarkin arewan Bauchi kuma fitaccen dan siyasa a jihar Bauchi a jam’iyyar APC, Alhaji Hassan Muhammad Sharif sun tabbatar da rasuwarsa sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan babban hanyar zuwa Abuja.

Ambasada Khalid Arewa dan mamacin ne ya tabbatar da rasuwar na mahaifinsu a hirarsa da wakilinmu wajajen karfe 10:00 na daren nan.

Ya ce, bayan da suka je asibitin da aka kwantar da shi a garin Akanga da ke jihar Nasarawa ne Likitoci suka tabbatar musu da rasuwar na mahaifin nasu.

Shi dai Alhaji Hassan Muhammad Sharif mamba ne cikin kwamitin yakin neman zaben dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar kuma mamba ne a kwamitin yada labarai na jam’iyyar APC a jihar Bauchi.

Bayanin hatsarin na Alhaji Hassan dai tun da yammacin yau ya yi ta karade kafafen sadarwar zamani sai dai babu tabbacin rasuwar har sai cikin daren nan.

Ahlin mamacin sun ce za su sanar da lokacin  yi masa Jana’iza a ranar Litinin.