Yadda hare-haren ‘yan bindiga ya mayar da garuruwa fiye da 50 kufai a Zamfara

0
111

Har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da tabarbarewa a garuruwa da dama na yankunan kananan hukumomin Gumi da Bukkuyum na Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Yanzu haka fiye da garuruwa 50 na neman zama kufai a yankunan kananan hukumomin sakamakon yadda hare-haren ‘yan bindiga suka tilasta wa jama’ar garuruwan yin gudun hijira zuwa wasu sassan jihar da makwaftan jihohi.

Hakan kuma na aukuwa ne duk da kudaden haraji fiye da naira miliyan dari da ‘yan bindigan suka karba daga hannun mutanen garuruwan, bisa yarjejeniyar ‘yan bindigan za su bari a gudanar da ayyukan noma, a kuma girbe kayan amfanin gona.

Mannir Sani Fura Girke, dan jarida nem ai binciken kwakwaf kan harkokin tsaro, ya shaida wa BBC cewa, na yi yarjejeniya da ‘yan bindigar da kuma garuruwa 55, inda suka yar da cewa ba zasu kara kai hare-hare ba muddin aka biya su kudin haraji.

BBCHAUSA