Hatsarin mota ya hallaka mutum 5 da raunata 2 a jihar Bauchi

0
121

A kalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku a kauyen Isma da ke kan babban hanyar Bauchi zuwa Jos a ranar Asabar, hatsarin ya jikkata mutum biyu.

Kwamandan shiyya na hukumar kiyaye aukuwar hadura (FRSC) a jihar Bauchi, Malam Yusuf Abdullahi shi ne ya tabbatar da hakan wa ‘yan jarida a jiya, yana mai cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 7:50 na safiya kuma ya rutsa da mutane bakwai, manyan maza uku, manyan mata uku gami da wata karamar yarinya.

Yusuf ya ce: “An samu aukuwar wani mummunar hatsari a kauyen Isma da ke kan hanyar Bauchi zuwa Jos a yau (Asabar), 5 ga watan Nuwamban 2023 wajajen karfe 7.50am.”

Ya kara da cewa hatsarin ya faru ne a tsakanin wata motar gida Peugeot 406 mai lamba: KRD649CA da kuma wata babbar motar tankar dakon Mai mallakin kamfanin Mai ta AIB mai lamba: MSA394SA.

A fadinsa, hatsarin ya faru ne sakamakon kauce wa ka’idojin tuki da tsula gudun wuce kima, kana motocin da kadarorin da aka kwaso a wajen da hatsarin ya faru an mika su ga sashin kula da cinkoson ababen hawa ta caji ofis din hukumar ‘yan sanda da ke GRA a Bauchi.

Ya daura da cewa, “Cikin gaggawa bayan da hatsarin ya wakana, jami’anmu sun garzaya inda abun ya faru cikin mintina 26 da sanar mana, sun kwashi wadanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa ta jami’ar ATBU domin nema musu kulawar likitoci.

“A nan ne likita ya tabbatar da mutuwar mutum biyar a cikinsu, maza biyu, mata biyu da wata yarinya.

“Sauran na miji da macen (Dukka manya) sun gamu da raunuka daban-daban kuma suna amsar kulawar likitoci, an kuma ajiye gawarwakin da suka mutu a dakib adana gawarwai amma daga baya za a mika su ga ahlinsu domin yi musu jana’iza,” ya shaida.