Hare-haren Rasha sun jefa kashi 10 na Ukraine a halin rashin lantarki- Zelensky

0
122

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce kashi 10 cikin 100 na al’ummar kasar yanzu haka na rayuwa ba lantarki sakamakon hare-haren Rasha da suka yi illa ga turakun wutar lantarki.

A jawabin kai tsaye da Zelensky ya gabatar ta video ya ce al’ummar kasar miliyan 4 da dubu 500 yanzu haka basu da lantarki a gidajensu saboda barnar da Rasha ta yi a yankunansu.

A cewar shugaban yankunan kasar 10 ne katsewar lantarkin ta shafa inda ya yi kira gas ashen lantarkin kasar da ya yi kokarin tattala lantarkin kasar don ganin al’umma na rayuwa a cikin haske tare da katse lantarkin wuraren da babu mutanen da ke rayuwa a wajen.

Shugaban na Ukraine ya bukaci katse lantarkin shagunan siyayya bayan rufewa da kuma allunan hanya masu amfani da lantarki don samun wadatuwar lantarkin ga sauran sassan kasar.

Zelensky cikin jawabin nasa ya yi kakkausar suka ga matakin Rasha na sauya matsuguni ga wasu al’ummomin Ukraine da ke rayuwa a yankunan da Moscow ta kwace iko da su.