Kungiyar afenifere ta yi amai ta lashe

0
96

Gamayyar kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere ta yi amai ta lashi, inda a baya ta bayyana cewa tana bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, saboda adalci, bin gaskiya da kuma rashin danne wani sashi na mika mulki ga yankin kudu maso gabashin Najeriya, amma kuma a yanzu ta bayyana cewa tana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyatr APC, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.

Shugabannin kungiyar Afenifere a dukkan fadin yankin kudu maso yamma ciki har da jihohin Kwara da Kogi sun bayyana goyan bayansu a gidan shugaban kungiyar, Pa Reuben Fasonranti da ke Akure, Babban Birnin Jihar Ondo.

Sun dai dauki wannan matakin ne bayan ganawa da Tinubu wanda ya ziyarci jihar domin gabatar da manufofinsa na sake fasalin Nijeriya.

Tinubu ya bayyana wa shugabannin Yarbawa cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin APC da ke arewa da sauran shugabannin yankin arewa sun yi Imani da cewa shi ne zai iya ceto Nijeriya daga kalubalan da ke fuskanta a halin yanzu.

Da yake gabatar wa shugabannin Yarbawan kundin manufofinsa na samar da ingantacciyar Nijeriya, Tinubu ya jaddada musu cewa za a samu ingantacciyar Nijeriya.

Idan za a iya tunawa dai lokacin da ya ziyarci Pa Fasoranti a ranar 4 ga watan Maris na wannan shekara kafin zaben fid da gwani na jam’iyyar APC, Tinubu ya yi wa shugaban kungiyar Afenifere alkawarin cewa zai dawo a lokacin da ya samu tikitin takarar shugaban kasa.

Tinubu ya ce ya zo Ondo ne domin ya cika alkawarin da ya dauka a baya, inda ya bukaci shugabannin Yarbawan su gode wa Shugaba Buhari da gwamnonin arewa bisa ba shi dama a jam’iyyarn APC.

Tsohon gwamna Jihar Legas ya ce, “’Yan arewa sun tabbatar mun da cewa zan iya hada kan Nijeriya. Wasu sun yi kokarin zuwa wurin Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin gabatar da wani, amma shugaban ya ki amincewa da bukatarsu, inda ya dage sai an bi tsarin yadda dimokuradiyya ya shimfida. Shugaban ya ce duk wanda zai daga martabar jam’iyyar APC shi ne ya cancanta. Daga baya dai ya karkara zuwa ga gaskiya.

“Gwamnonin APC na arewa su suka dage dole sai mulki ya je yankin kudu, musamman ma kudu maso yamma. Gwamna Nasir El-Rufai da Abdullahi Ganduje da sauransu su suka goya min baya daga karshe,” in ji Tinubu.

Tun da farko dai, sakatare janar na kungiyar Afenifere, Cif Seinde Arogbofa ya bukaci Tinubu ya zama shugaban kasa domin hada kan Nijeriya da aiki tukuru wajen inganta kasa baki daya.

Ya ce, “Ba wai za ka kasance shugaban Yarbawa ba ne kadai, sai dai shugaban Nijeriya gaba daya. Lokacin da ka zama shugaban kasa, duk abin da za ka yi ka dunga tunawa da Nijeriya sannan kar ka manta da gida. Ka san irin bukatocinmu wadanda suka hada da samar da tsaro da inganta tattalin arziki. A yanzu haka kasarmu babu tsaro, muna bukatar ‘yansandan jihohi saboda tsaron kasarmu.”

Mataimakin gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa wanda shi ne ya tarbi Tinubu a madadin Gwamna Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa, mutanen Jihar Ondo da kungiyar Afenifere suna goyon bayan Tinubu ya zama shugaban kasa.

Sakamakon ganawar kungiyar Afenifere da Tinubu, mai magana da yawun tawagar yakin neman zaben Atiku/Okowa, Daniel Bwala ya bayyana cewa kamata ya yi kungiyar Afenifere ta gayyaci sauran manyan ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba wai na APC kadai ba.

“Na yi tsammanin Afenifere za ta gayyaci manyan ‘yan takara guda hudu kamar yadda kungiyar arewa ta yi, amma sai ta gayyaci Tinubu kawai,” in ji shi.

Da yake mayar da martani game da goyon bayan Tinubu, Bwala ya ce kasancewa rashin halartar ganawar da wasu jiga-jigan ‘yan kungiyan kamar irinsu Pa Ayo Adebanjo da Cif Sola Ebiseni ya nuna goyon ba halattacce ba ne.

Bwala ya siffanta Tinubu a matsayin wanda yake kokarin amfani da kabilanci domin ya samu nasara.