An kashe ‘yan bindiga a cikin kasuwa a Zamafara

0
106

‘Yan sintiri sun harbe ‘yan bindiga biyu bayan sun kai hari a kasuwar Gidan Goga da ke Karamar Hukumar Maradun a Jihar Zamafara.

Wani mazauni a yankin ya ce gungun ‘yan bindigar sun kai hari ne a kasuwar wadda take da nisan kilo mita bakwai a hanyar Kaura Namoda zuwa Shinkafi, inda suka fara harbe-harbe, inda wasu mutum uku da suka yi kokarin arcewa, ‘yan bindigar suka harbe su.

Ya ce, “‘Yan sintirin sun yi amfani da bindigarsu ta baushe wajen harbe ‘yan bindigar, inda hakan ya sa suka samu nasarar kashe ‘yan bindiga biyu a nan take.

“‘Yan sintirin sun sake sauya matsayarsu suka ci gaba da zaman wuta a yankin da ‘yan bindigar ke yunkurin guduwa.

“Dga baya, ‘yan sintirin sun bukaci a kawo musu daukin jami’an tsaro, inda jami’an tsaron suka isa kasuwar wadda akasarin ‘yan kasuwar tuni sun tsere, bayan da ‘yan bindigar suka saci hatsi suka kuma banka wa babura wuta.

Mazaunin yankin ya ce, jami’an tsaron, sun kuma gano wasu kakin soji da sauran kayan da gungun ‘yan bindigar suka arce suka bari, inda daya daga cikin ‘yan kasuwar da aka kashe wanda ya fito daga Kaura Namoda aka tsara za yi masa zana’ida gobe da safe.

Har zuwa hada wannan rahoton, kakakin rundunar ‘yansanda na jihar SP Muhammad Shehu, bai fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.