Ma’aikatan N-Power sun yi zanga-zangar kin biyansu hakkokinsu a Bauchi

0
127

Tsofaffun wadanda suka ci gajiyar shirin N-Power karkashin shirin NSIP na gwamnatin tarayya a jihar Bauchi a Laraba sun gudanar da zanga-zangar lumana kan rashin biyansu kudaden da aka yi musu alkawarin za a basu su fara sana’o’i.

Shugaban masu cin gajiyar shirin N-Power na kasa, Bashir Usman Gobir, ya shaida wa manema labarai yayin zanga-zangar cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta cika musu alkawarin da ta yi musu ta hannun ma’aikatar jin kai da ci gaban al’umma ta tarayya tare da hadin gwiwar babban bankin Nijeriya.

A watan Maris na wannan shekarar, ma’aikatar ta shirya wani horo kan harkokin kasuwanci ga wadanda suka ci gajiyar shirin, inda tayi musu wannan alkawarin.

Ya ce an umarce su da su nuna shirinsu na kasuwanci a rubuce tare da alkawarin za a ba su kudade domin fara kasuwanci da zasu dogara da kansu.

Gobir ya ce, “Mu 500,000 da muka ci gajiyar shirin a zagayen A da B na shirin da ma’aikatar jin kai ta yi a shekarar 2016 da 2017, ya kamata a ba mu kudaden da aka alkawarta mana na fara sana’o’in da za mu zama masu dogaro da kai.