Tsohon dan wasan kwallon kafa na Kano Pillars, Kofarmata, ya rasu

0
147

Allah ya yiwa tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Bello Musa Kofarmata.

Ya rasu ne a daren ranar Talata yana da shekara 34 a duniya bayan wata yar gajeruwar rashin lafiya da ta sameshi a gidansa da ke unguwar Kofarmata a jihar Kano.

Tsohon mataimakin shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni na shiyyar Arewa Maso Yamma, Ado Salifu shi ne ya tabbatar wa LEADERSHIP rasuwar, ya ce, tunin aka yi jana’izar mamacin da safiyar ranar Laraba kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a Kofarmata da ke Kano.

Kofarmata dai ya shiga kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ce a shekarar 2007 ya kuma taimaka wa kungiyar wajen samun nasara a yayin gasar Premier league ta Nijeriya da aka gudanar 2007/2008 da kwallaye 11. Kuma shi ne wanda ya fi zura kwallaye da suka kai su ga nasara.

Ya bar kungiyar Kano Pillars a shekarar 2010 inda ya shiga kungiyar kwallon kafa ta Heartland FC da ke Owerri daga baya ya sake barinta a shekarar 2012 kuma ya shiga kungiyar Elkanemi Warriors da ke Maiduguri.