EFCC ta kama ɗan takarar majalisa ɗauke da naira miliyan 326, da dala 610,500 a jihar Kogi

0
144

Hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da ɗan takarar majalisar dokokin jihar Kogi na jam’iyyar NNPP a kotu.

Hakan ya biyo kama ɗan takarar ai suna Ismaila Yusuf Atumeyi da tsabar kuɗi naira miliyan 326 da kuma dalar Amurka 140,500.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren ya ce sun kama Atumeyi, wanda ke takarar ɗan majalisa mai wakiltar gundumar Ankpa 11 ne a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, 2022.

Ya kuma ce sun samu nasarar kama wani mai suna Joshua Dominic, wanda ake zargi da zamba, a lokacin wani samame da suka kai a yankin Karsana, da ke unguwar Gwarimpa, na birnin tarayya, Abuja.