Babu barazanar kai hari a Kano – ‘Yan sanda

0
122

Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta karyata labarin wani harin ta’addanci da aka kai a Kano a matsayin labarin karya.

Leadership Hausa ta rawaito cewar labarin harin ta’addanci ya samo asali ne daga wata kafar yada labarai ta yanar gizo.

Sai dai wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan Kano, SP Abdullahi Haruna ya fitar, ya ce babu wani harin ta’addanci da aka kai.

Haruna, wanda ya bayyana labarin a matsayin wanda ba gaskiya ba ne, ya danganta lamarin ga marubuta na son kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake samu a jihar a halin yanzu.

SP Haruna ya umarci mazauna Kano da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na yau da kullum ba tare da fargaba ba, inda ya ce tuni rundunar ta tsara dabarun tabbatar da tsaro a jihar.

Ya ce ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro a shirye suke domin dakile duk wani yunkuri da ‘yan ta’adda za su iya kai wa na kawo rudani a jihar.