Darajar Naira na cigaba da faduwa warwas

0
113

Darajar Naira na ci gaba da faduwa yayin da farashin Dala a kasuwar bayan fage ya kai Naira 818 a ranar Litinin.

Binciken Daily Trust ya nuna cewa faduwar darajar Naira bai rasa nasaba da sanarwar da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar na sauya fasalin kudin wanda za a kaddamar daga ranar 15 ga watan Disamba 2022.

Bayan wannan sanarwa a makon da ya gabata, darajar Naira ta soma faduwa daga yadda ake canjar Dala daya a a kan N765 zuwa N818 a ranar Litinin, kuma da alama faduwar ba ta tsaya nan ba.

Aminiya ta ziyarci kasuwar ‘yan canji da ke Unguwar Zone 4 a Abuja, ta kuma ruwaito yadda mutane da yawa suke sintirin neman Dalar, amma ta yi wahala.

Wakilinmu da ya zaga wurin wasu ‘yan canjin a matsayin mai saye, ya ce yana son $10,000, amma babu wani mai canjin da ya ke da wannan adadin da zai sayar, wasu cewa su ka yi ba su da ko $5,000.

Wani dan canji mai suna Isma’ila Yusuf ya bayyana cewa, Dala na matukar wahala, kuma ba da dadewa ba jami’an EFCC su ka zo kamen wadanda suka zo sayen Dalar mai yawa.

Sai dai ya ce, ‘yan canjin na taka tsantsan wajen sayar da Dalar mai yawa ga mutane a yanzu.

Kawo yanzu dai ba a iya tabbatar da musabbabin karancin dalar, inda ake zargin boyeta ‘yan canji suke yi domin cin kazamar riba, ko kuma da gaske karancinta ake yi.