Jirgin kasan Abuja zai soma aiki nan ba da dadewa ba

0
88

Jirgin kasan da zai rika jigila a cikin Babban Birnin Tarayya na Abuja don rage wahalar zirga-zirga zai soma aiki nan ba da dadewa ba.

Ministan Abuja, Malam Muhammadu Bello ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara Kamfanin CCECC da ke kwagilar samar da kuma gudanar da aikin jirgin.

Yayin ziyarar an zagaya da ministan da ayarinsa lungu da sako na cibiyar gudanar ayyuka da kuma sarrafa jirgin da ke Idu, bayan wata ganawa da manyan jami’an kamfanin.

A jawabin Babban Sakataren Hukumar FCTA Mista Olusade Adesola ya ce, makasudin ziyarar shi ne, su duba inda aka kwana dangane da aikin jirgin da kuma inda za a dora dangane da shirin soma aikin jirgin.

Mista Adesola ya ce hukumar ta kashe kudi mai yawa, da kuma tallafin Gwamnatin Tarayya har an kai ga matakin soma gwajin jirgin kafin annobar COVID-19 ta bulla, lamarin da ya ta tilasta dakatar da aikin.

“Yanzu annobar COVID-19 ta wuce, kuma muna da bukatar jirgin nan ya soma aiki cikin lokaci kankani…” in ji Mista Adesola.

Dangane da batun tsaro, Babban sakataren ya yi bayanin cewa, an tanadin cikakken tsarin tsaro ga jirgin tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro na birnin.