Ba mu san inda A.A Zaura ya shiga ba – EFCC

0
115

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta ce ba ta san inda dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na jam’iyyar APC, Abdussaalam Abdulkarim (A.A. Zaura), ya shiga ba.

 

EFCC ta shaida hakan ne a gaban Babbar Kotun Jihar Kano, wacce aka gurfanar da dan siyasar bisa zarginsa da hannu a badakalar damfarar wani dan kasar Kuwait kudaden da suka kai Dalar Amurka miliyar daya da dubu 300, a gaban kotun.

An dai shirya dawo da ci gaba da sauraron karar ce a ranar Litinin, bayan Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da umarnin sakinsa tare da sake shari’ar.

To sai dai wanda ake tuhumar bai bayyana a gaban kotun ba ranar Litinin, kamar yadda ya yi ranar 14 ga watan Oktoba, ranar da aka tsara gurfanar da shi.

 

To sai dai da take amsa tambayar da alkalin kotun ya yi mata, lauyar EFCC, Aisha Habib, ta ce sam ba su san inda A.A. Zauran ya shiga ba, kuma hakan raini ne babba ga kotun.

To sai dai lauyan dan siyasar, Ibrahim Waru, ya ce ba lallai sai wanda yake karewar ya bayyana a gaban kotun ba kasancewar sun shigar da wata karar suna kalubalantar hurumin kotun na sauraron karar.

Kazalika, ya ce wanda yake karewar ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai iya tsayawa a gaban kotun, kuma suna da shaidar asibiti a kan hakan.

 

Daga nan ne Alkalin kotun, Mai Shari’a Mohammed Nasiru Yunusa, ya bayar da umarnin a a kawo rubutacciyar shaidar da za ta nuna cewa wanda ake tuhumar ba shi da lafiya a matsayin dalilinsa na kaurace wa kotun.

Ya kuma dage ci gaba da sauraron karar har zuwa nan da ranar 10 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Idan za a iya tunawa, a watan Yunin 2020 ce wata kotun da Mai Shari’a Lewis Allagoa na kotun ya wanke A.A. Zaura tare da korar karar.

Sai dai bayan rashin gamsuwa da hukuncin, EFCC ta sake daukaka kara tana neman a sake duba shari’ar.