Gwamnatin sojin Mali ta mayar da ‘yan sandan kasar karkashin rundunar soja

0
83

Gwamnatin mulkin Sojin Mali ta mayar da ‘yan sandan kasar karkashin rundunar sojojinta, a kokarin da take yi na murkushe ‘yan ‘ta’adda masu ikirarin Jihadi, wadanda suka shafe shekaru akalla 10 suna addabar sassan kasar.

Gwamnatin sojin kasar ta Mali ta ce matakin zai ba ta damar jibge ‘yan sandan a yankunan da sojoji suka kwato daga hannun ‘yan ta’adda, domin tabbatar da tsaron jama’a da dukiyarsu, da kuma dakile duk wani yunkuri na masu ikirarin jihadi ko ‘yan tawaye sake mamaye yankunan da suka subuce musu.

Tun daga shekarar 2020 ne sojoji ke mulkin kasar Mali.

Majalisar zartaswar kasar ta rikon kwarya ce kuma ta CNT wadda sojojin da suka yi juyin mulki suka kafa ta zartar da dokar baiwa jami’an tsaro na ‘yan sanda kayan aikin sojoji mako guda da ya gabata.

Sai dai tun kafin amincewa da aiwatar da matakin mayar da su karkashin rundunar sojoji kungiyoyin ‘yan sandan suka soki manufar da suka bayyana a  matsayin shawarar da bangare daya yayi gaban kansa wajen zartaswa.