Gwamnatin Gombe ta dauki ma’aikatan lafiya 451 aiki

0
130

Gwamnatin jihar Gombe ta dauki ma’aikatan kiwon lafiya 440 aiki domin sake fasalin fannin kiwon lafiya domin samar da ingantaccan aiki.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai na gidan gwamnati Ismaila Misili kuma aka rabawa manema labarai a Gombe ranar Asabar.

Ya ce jami’an da aka dauka sun hada da Ugozoma 106, Ma’aikatan Lafiyar Jama’a 213 (CHEW), Kananan Ma’aikatan Kiwon Lafiyar Jama’a 132 (JCHEW) wadanda za a tura su cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a fadin jihar.

Ya ce za a tura sabbin ma’aikatan zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a fadin jihar

“Wannan saboda gwamnatin yanzu ta Gwamna Inuwa Yahaya ta yi imanin cewa kiwon lafiya a matakin farko shine tushen tsarin kiwon lafiya,” in ji shi.

Ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta ba da fifiko ga harkokin kiwon lafiya da walwalar ‘yan kasa, don haka aka samu dimbin jari a bangaren.

Ya ce daukar ma’aikata wani babban abin tarihi ne a tarihin wannan fanni a jihar, baya ga fara aikin gida a asibitin kwararru, da hada hadar kwararrun masu ba da shawara.

Misili ya ce fara horar da zama da kuma ci gaba da gina sabuwar kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da ke Gombe duk sun yi nisa ne domin inganta aikin dan Adam na kiwon lafiya a jihar.