Ƴan mata sun tafi yajin aikin zance da samari sabo da rashin wutar lantarki a Kano

0
122

Ƴan mata a unguwar Kuntau da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a jihar Kano sun ce ba za su sake yin zance da samarinsu ba har sai an gyara matsalar wutar lantarki a yankin nasu.

Freedom Radio ta rawaito cewa mazauna unguwar sun koka kan yadda su ka shafe watanni takwas ba tare da samun wutar lantarki ba, sakamakon lalace wa da na’urar bada wutar lantarki, wato ‘transfomer’ ta yi.

Mazuna unguwar sun ce duk koken da su ka kai wa kamfanin rarraba wutar lantarki na jiha, KEDCO, abin ya ci tura, inda hakan ya haifar musu da nakasu a harkokin rayuwarsu, a cewar mazauna unguwar.

Su ma ƴan matan unguwar sun ce tun da haka ne, to ba za su sake yin zance da samarinsu ba har sai an gyara musu wutar unguwar ta su.

A cewar ƴan matan, sun saba yin zance a hasken fitila, amma tun da babu wutar lantarki har tsawon watanni 8, to sun ma jingine yin zancen har sai wuta ta dawo.

Sun ce sun gaji da kunna fitila domin haskaka inda su ke yin zancen tunda dai samarin na su ba sa basu kuɗin sayen batir.

Freedom Radio ta ce ta tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na KEDCO, Ibrahim Shawai, wanda ya ce za su duba lamarin.