Sojojin Amurka sun kai samame wani rukunin gidaje a Abujan Najeriya

0
126

Sojojin Amurka da jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, sun kai samame a rukunin gidaje na Trademore da ke unguwar Lugbe a babban birnin tarayya Abuja.

An kai farmakin ne a daidai lokacin da ake kara tada jijiyoyin wuya kan yiwuwar harin ta’addanci a babban birnin kasar.

Amurka da Birtaniya sun yi gargadin yiwuwar kai harin ta’addanci a Abuja, musamman kan gine-ginen gwamnati da wuraren ibada da makarantu da dai sauransu.

Gwamnatocin Australia, Ireland da Canada suma sun nuna fargaba kan yiwuwar barazanar harin ta’addanci a babban birnin Najeriya.

A yayin farmakin da aka kai a rukunin gidaje na Trademore, an takaita zirga-zirga gaba daya, yayin da jami’an tsaro ke farautar masu tayar da kayar bayan.

Wata sanarwa da hukumar gudanarwar rukunin gidajen ta fitar, ta bukaci mazauna yankin da su kasance cikin taka tsan-tsan.

Rahotanni daga Najeriya sun ruwaito yadda jami’an tsaro ke bakin kokarinsu wajen ganin an dakile munanan hare-haren da ā€˜yan ta’adda masu biyayya ga kungiyar IS a yammacin Afirka ta ISWAP suke kokarin kaiwa Abuja da kewaye.

An gano shigar ā€˜yan ta’addan Abuja ya biyo bayan wani gagarumin aikin leken asiri ta sama da samamen da sojojin Najeriya suka yi a yankin arewa mai nisa na Borno mai iyaka da Chadi da Nijar da Kamaru da dazuzzukan Alagarno da Sambisa a Arewa maso Gabas, da kuma hare-haren bama-bamai a yankunan da ke da dazuzzuka a sassan kasar.