PDP ta musanta nada janar Bamaiyi a matsayin daraktan yakin zabe a Kebbi – Jam’iyya

0
106

Jam’iyyar PDP a jihar Kebbi ta musanta nada Janar Ishaya Bamaiyi a matsayin Darakta Janar na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar a yayin babban zaben 2023 da ke tafe.

Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Usman Bello-Suru, shi ne ya bayyana haka a Birnin Kebbi, babban birnin jihar yayin da yake mayar da martani ga wani rahoton yanar gizo da daya daga cikin jaridun nan kasa (Wacce ba namu ba) ta wallafa.

Wakilinmu LEADERSHIP ya ruwaito wannan labarin ya fito ne daga wani taron manema labarai da Alhaji Kabiru Tanimu-Turaki, Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP (BOT) kuma tsohon ministan ayyuka na musamman ne ya bayar a baya.

Alhaji Bello-Suru ya ce: “Hankalin jam’iyyar PDP a jihar Kebbi ya karkata ne ga wata hira da aka wallafa da Alhaji Kabiru Tanimu Turaki (SAN) ya yi da manema labarai kuma jaridar ta buga a dandalinta na yanar gizo mai taken: “PDP ta nada Janar Bamaiyi Darakta Janar na yakin neman zaben Atiku Abubakar a shugaban kasa na Jihar Kebbi”.

“Tattaunawar da aka yi a kafafen yada labarai da ake magana a kai da jama’a musamman ‘ya’yan jam’iyyar PDP na jihar Kebbi aka nada Janar Ishaya Bamaiyi a matsayin Darakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar Kebbi.

“Muna so mu bayyana cewa nadin ya wanzu ne kawai a cikin tunanin Kabiru Tanimu Tukari, SAN, amma ba da yawun Jam’iyyar a matakin jiha ko a Tarayya ba.”

Ya ce hakika an kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jihar Kebbi kamar yadda shugabannin jam’iyyar na kasa suka bayar a wata daya da ya gabata, inda ya kara da cewa majalisar yakin neman zaben shugaban kasa tana karkashin jagorancin Dakta Bello Haliru, wanda shi ne tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na kasa.

Shugaban ya ce bin umarnin hedkwatar kasa, “Duk jihar da ba jam’iyya ba ce, babban jigo a jam’iyyar ya zama shugaban kwamitin yakin neman zabe, yayin da mai rike da tuta na gwamna ya zama mataimakinsa, don haka Dakta Bello Haliru da Janar Aminu Bande mai ritaya su ne ke rike da Jagorancin shugabancin yakin neman zaben Shugaban kasa a Jihar.”

A cewarsa, Darakta Janar din jam’iyyar guda daya ne kawai, majalisar yakin neman zaben shugaban kasa, wanda shi ne Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato, yayin da Jihohi ke da shugabanni ba Darakta Janar ba .

Daga karshe Alhaji Usman Bello-Suru ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da labaran da aka wallafa a kafafen yada labarai, yana mai jaddada cewa PDP na nan daram a Jihar Kebbi domin kuwa Kabiru Tanimu-Turaki bai wakiltan kowa dangane da shugabanci.