Ba mu taba ganin ambaliyar ruwa mafi muni a Nijeriya kamar ta bana ba – Gwamnati

0
87

Gwamnatin tarayya ta bayyana irin yadda ambaliyar ruwa ta ta’azzara a bana a matsayin wacce bata taba ganin irinta ba.

Ministan Albarkatun Ruwa na kasa Injiniya Sulaiman Adamu ne ya bayyana hakan a gaban taron majalisar zartarwar kasa na mako-mako a ranar larabar da ta gabata.

Fiye da mutane 600 ne aka tabbatar sun mutu a hukumance a ambaliyar da ta shafi kashi biyu bisa uku na jihohin kasar 36.

A cewar gwamnatin, babban musabbabin wannan ibtila’i shi ne saukar ruwan sama fiye da yadda ake zato a daminar bana har ma a yankunan kasar wadanda ga al’ada suke da karancin ruwan sama saboda kusancinsu da hamada.

A nasa jawabin gaban manema labarai ministan ayukkan da gidaje na Najeriyar Babatunde Fashola ya ce ya shaidawa majalisar cewa ambaliyar talalata hanyoyi da gadoji sama da 150 a duk fadin kasar abin da ke bukatar zunzurutun kudi har Naira biliyan 80 kafin a gyara su. A wani rahoto da BBC Hausa ta nakalto.