Newcastle ta shiga jerin kungiyoyi hudu na farko a Firimiya

0
111

Kungiyar Newcastle ta kai zuwa mataki na hudu a teburin gasar Firimiya, bayan doke Tottenham har gida da kwallaye 2-1, yayin karawar da suka yi a ranar Lahadi.

Bayan busar karshe, ‘yan wasa da magoya bayan kungiyar ta Newcastle sun yi ta sowar nuna farin ciki kan nasarar da suka samu, sakamakon fatan da suka karfafa na yiwuwar samun halartar gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a kaka mai zuwa, idan har suka kare kakar wasa ta bana da kwazon da suka fara.

Karo na farko kenan da Newcastle ta shiga jerin kungiyoyi hudu na farko a gasar Firmiya bayan buga wasanni 12, bajintar da rabon da ta yi, tun shekarar 2012.

Rabon da Newcastle ta haska a gasar Zakarun Turai tun kakar wasa ta shekarar 2012/2013, inda ta gaza tsallaki matakin rukuni.