Kwankwaso ya yi bikin cikarsa shekaru 66 a duniya

0
86

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Dr Rabi’u Kwankwaso, a ranar Asabar ya kaddamar da wata cibiyar shugabanci a Kano domin bikin cikarsa shekaru 66 a duniya.

A yayin bikin, tsohon gwamnan na Kano ya ce Cibiyar jagoranci ta Amana za ta gudanar da shirye-shiryen gidauniyar kan bunkasa hankali da tunanin dan adam.

A cewarsa, “Cibiyar tana da alaƙa da cibiyoyin koyo na ƙasa da ƙasa a Burtaniya, Indiya da Asiya.
“Za ta gudanar da jarrabawar hukumar hadin gwiwa ta wucin gadi (IJMB), domin baiwa matasa damar shiga jami’o’in Najeriya da na kasashen waje domin samun cigaban matasa,”

Kwankwaso ya yi kira ga al’ummar Kano da su yi amfani da Cibiyar ta hanyar da ta dace.
A lokacin da yake jawabi a wajen taron, dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar NNPP a Kano ta tsakiya, Sen. Rufa’i Hanga, ya yabawa Kwankwaso bisa wannan gagarumar nasara da ya samu.

Ya kuma yi kira ga sauran ‘yan siyasa da su yi koyi da Kwankwaso, ta hanyar gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwarsu da ayyuka masu amfani maimakon tafiya kasashen waje.

Ya bayyana fatansa na cewa Cibiyar za ta tsara shugabannin da ke tafe tare da samar da ingantaccen ilimi ga dalibai.