Kayan abinci sun yi tashin gauron zabi saboda ambaliyar ruwa a Najeriya

0
89

Farashin kayayyakin abinci ya yi tashin goron-zabbi a Najeriya musamman a yankin kudancin kasar sakamakon matsalar ambaliyar ruwa wadda ta haifar da cikas wajen safarar abincin daga arewacin kasar zuwa kudanci, al’amarin da ke kara jefa jama’a cikin halin ni-‘yasu.

Ambaliyar wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 600 tare da raba miliyan biyu da muhallansu, ta haddasa asara ga ‘yan kasuwa da ke safarar hajojinsu daga arewa zuwa kudanci sakamakon yadda ta mamaye hanyoyin da motoci suka saba ratsawa.

Wani bincike da Jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa, farashin kayayyakin abinci da suka hada da tumatur da masara da shinkafa da wasu nau’uka na hatsi ya yi tsada matuka musamman a jihohin Lagos da Ogun saboda karancin manyan motocin da ke shigar da kayan cikin jihohin.

Rahotanni na cewa, buhun masara da aka saba sayar da shi akan Naira dubu 15, yanzu ya koma Naira dubu 29, yayin da wasu ‘yan kasuwa ke cewa, muddin aka gaza daukar matakin gaggawa, to akwai yiwuwar kasar baki daya ta tsunduma cikin matsalar karancin abinci.

Tuni dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta aika da tallafin abinci da suka hada da masara da dawa da garin-rogo ga gwamnatin jihar Lagos domin rage wa al’umma radadin karancin abincin.

Kazalika gwamnatin tarayyar ta hannun Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasar, NEMA ta tallafa wa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa da kayayyakin amfanin yau da kullum har da abinci.

Gagarumar ambaliyar ruwan da ta mamaye garin Lokoja da ke jihar Kogi ta haifar da mummunan koma-baya ga zirga-zirgar motoci da ke safara tsakanin arewacin kasar zuwa kudanci, yayin da manyan motocin dakon-kaya suka makale a cikin garin na Lokoja, inda suka shafe makwanni ba-gaba-ba-baya.

Rahotanni na cewa, yanzu haka motocin dakon-kaya daga jihar Kano na ratsawa ne ta kasar Nijar zuwa kasar Benin kafin daga bisani su dawo ta kan iyakar Seme domin shiga cikin jihar Lagos da ke kudancin Najeriya.